Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

2 Kor 5:9-15 Littafi Mai Tsarki (HAU)

9. Saboda haka, ko muna gunsa, ko muna a rabe da shi, burinmu shi ne mu faranta masa zuciya.

10. Don lalle ne a gabatar da mu duka, a gaban kursiyin shari'a na Almasihu, domin kowa yă sami sakamakon abin da ya yi tun yana tare da wannan jiki, ko mai kyau ne, ko kuma marar kyau.

11. Da yake muna tsoron Ubangiji, shi ya sa muke ƙoƙarin rinjayar mutane. Yadda muke kuwa, ai, sananne ne ga Allah, muna fata ku ma haka abin yake a lamirinku.

12. Har wa yau kuma, ba yabon kanmu muke yi a gare ku ba, sai dai muna ba ku hanyar yin taƙama da mu, don ku sami yadda za ku mai da jawabi ga waɗanda suke fariya da maƙaminsu, ba da halinsu ba.

13. In hankalinmu ya fita, ai, saboda Allah ne, in kuwa a cikin hankalinmu muke, ai, ribarku ce.

14. Ƙaunar Almasihu a gare mu, ita take mallakarmu, saboda haka mun tabbata, da yake wani ya mutu saboda dukan mutane, ashe kuwa, mutuwarsu ce dukansu.

15. Ya kuwa mutu ne saboda dukan mutane, domin waɗanda suke a raye, kada su yi zaman ganin dama a nan gaba, sai dai su yi zaman wannan da ya mutu saboda su, aka kuma tashe shi saboda su.

Karanta cikakken babi 2 Kor 5