Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

2 Kor 5:11-19 Littafi Mai Tsarki (HAU)

11. Da yake muna tsoron Ubangiji, shi ya sa muke ƙoƙarin rinjayar mutane. Yadda muke kuwa, ai, sananne ne ga Allah, muna fata ku ma haka abin yake a lamirinku.

12. Har wa yau kuma, ba yabon kanmu muke yi a gare ku ba, sai dai muna ba ku hanyar yin taƙama da mu, don ku sami yadda za ku mai da jawabi ga waɗanda suke fariya da maƙaminsu, ba da halinsu ba.

13. In hankalinmu ya fita, ai, saboda Allah ne, in kuwa a cikin hankalinmu muke, ai, ribarku ce.

14. Ƙaunar Almasihu a gare mu, ita take mallakarmu, saboda haka mun tabbata, da yake wani ya mutu saboda dukan mutane, ashe kuwa, mutuwarsu ce dukansu.

15. Ya kuwa mutu ne saboda dukan mutane, domin waɗanda suke a raye, kada su yi zaman ganin dama a nan gaba, sai dai su yi zaman wannan da ya mutu saboda su, aka kuma tashe shi saboda su.

16. Saboda haka, a nan gaba ba mā ƙara duban kowane mutum bisa ga ɗabi'ar jiki kawai, domin ko da yake mun taɓa duban Almasihu bisa ga ɗabi'ar jiki, yanzu ba ma ƙara dubansa haka.

17. Saboda haka, duk wanda yake na Almasihu sabuwar halitta ne, tsohon al'amari duk ya shuɗe, ga shi, kome ya zama sabo.

18. Duk wannan kuwa yin Allah ne, shi da ya sulhunta mu da kansa ta wurin Almasihu, ya kuma ba mu aikin shelar sulhuntawar,

19. wato, Allah ne, ta wurin Almasihu, yake sulhunta 'yan adam da shi kansa, ba ya kuwa lasafta laifofinsu a kansu ba, ya kuma danƙa mana maganar nan ta sulhuntawa.

Karanta cikakken babi 2 Kor 5