Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

2 Kor 4:9-18 Littafi Mai Tsarki (HAU)

9. Ana tsananta mana, duk da haka ba mu zama yasassu ba. Ana ta fyaɗa mu a ƙasa, duk da haka ba a hallaka mu ba.

10. Kullum muna a cikin hatsarin kisa, irin kisan da aka yi wa Yesu, domin a bayyana rayuwar Yesu ta gare mu.

11. Wato, muddin muna a raye, kullum zaman mutuwa muke yi saboda Yesu, domin a bayyana ran Yesu ta wurin jikin nan namu mai mutuwa.

12. Ta haka mutuwa take aikatawa a cikinmu, ku kuwa rai a cikinku.

13. Tun da yake muna da ruhun bangaskiya iri ɗaya da na wanda ya rubuta wannan, “Na gaskata, saboda haka na yi magana,” to, mu ma mun gaskata, saboda haka kuma muke magana.

14. Mun sani shi wannan da ya ta da Ubangiji Yesu daga matattu, mu ma zai tashe mu albarkacin Yesu, yă kuma kawo mu a gabansa tare da ku.

15. Duk wannan fa don amfaninku ne, domin alherin Allah ya yaɗu ga mutane masu yawa, ta haka ya zama sanadin yawaita godiya ga Allah, domin a ɗaukaka Allah.

16. Saboda haka ba mu karai ba, ko da yake jikinmu na mutuntaka yana ta lalacewa, duk da haka, ruhunmu a kowace rana sabunta shi ake yi.

17. Don wannan 'yar wahalar tamu, mai saurin wucewa ita take tanadar mana madawwamiyar ɗaukaka mai yawa, fiye da kwatanci.

18. Domin ba abubuwan da ido yake gani muke dubawa ba, sai dai marasa ganuwa, gama abubuwan da ake gani, masu saurin wucewa ne, marasa ganuwa kuwa, madawwama ne.

Karanta cikakken babi 2 Kor 4