Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

2 Kor 2:14-17 Littafi Mai Tsarki (HAU)

14. Amma godiya ta tabbata ga Allah, shi da kullum yake yi mana jagaba mu ci nasara, albarkacin Almasihu, ta wurinmu kuma yake baza ƙanshin nan, na sanin Almasihu a ko'ina.

15. Don kuwa, a gun Allah mu ne ƙanshin Almasihu a cikin waɗanda ake ceto, da waɗanda suke a hanyar hallaka.

16. Ga na ƙarshe ɗin, ƙanshin nan warin mutuwa ne, mai kaiwa ga hallaka, ga na farkon kuwa, ƙanshin rai ne mai kaiwa ga rai. To, wa zai iya ɗaukar nauyin waɗannan abubuwa?

17. Domin mu ba kamar mutane da yawa muke ba, masu yi wa Maganar Allah algus, mu kaifi ɗaya ne, kamar yadda Allah ya umarce mu, haka muke magana a gaban Allah, muna na Almasihu.

Karanta cikakken babi 2 Kor 2