Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

2 Kor 11:26-33 Littafi Mai Tsarki (HAU)

26. Na yi tafifiya da yawa, na sha hatsari a koguna , na sha hatsarin 'yan fashi, na sha hatsari a hannun kabilarmu, na sha hatsari a hannun al'ummai, na sha hatsari a birane, na sha hatsari a jeji, na sha hatsari a bahar, na kuma sha hatsarin 'yan'uwa na ƙarya.

27. Na sha fama, na sha wuya, na sha rashin barci, na sha yunwa da ƙishirwa, sau da yawa na rasa abinci, na sha sanyi da huntanci.

28. Banda waɗansu abubuwa dabam kuma, kowace rana ina a matse da matsananciyar kula saboda dukan ikilisiyoyi.

29. Wane ne ya raunana da ban raunana ba? Wane ne aka sa tuntuɓe, ban ji zafin ba?

30. In ma lalle ne in yi gadara, to, sai in yi taƙama da abubuwan da suke nuna raunanata.

31. Allahn Ubangiji Yesu, wato Ubansa, wanda ya yabo ya tabbata a gare shi har abada, ya sani ba ƙarya nake yi ba.

32. A Dimashƙu gwamnan da yake ƙarƙashin sarki Aretis ya tsare ƙofofin birnin Dimashƙu don ya kama ni,

33. amma sai aka zura ni a cikin babban kwando ta tagar garu, na kuɓuce masa.

Karanta cikakken babi 2 Kor 11