Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

2 Kor 1:13-24 Littafi Mai Tsarki (HAU)

13. Domin wasiƙarmu zuwa gare ku, ba ta ƙunshi wani abu dabam ba, sai dai ainihin abin da kuka karanta kuka kuma fahimta, ina kuwa fata ku fahimta sosai da sosai,

14. kamar yadda kuka riga kuka ɗan fahimce mu, cewa kwa iya yin fāriya da mu, kamar yadda mu ma za mu iya yi da ku, a ranar Ubangijinmu Yesu.

15. Saboda na amince da haka, shi ya sa na so zuwa wurinku da fari, domin ku sami albarka riɓi biyu.

16. Wato niyyata in bi a kanku in za ni Makidoniya, in kuma komo wurinku daga Makidoniya, sa'an nan ku yi mini rakiya in zan tafi Yahudiya.

17. Ashe, a lokacin da na yi niyyar yin haka, wato na nuna rashin tsai da zuciya ke nan? Ko kuwa shiririta nake yi kawai irin ta halin mutuntaka, in ce, “I” in koma in ce, “A'a”?

18. Yadda ba shakka Allah yake mai alkawari, haka ma maganar da muka yi muku, ba shiririta a ciki.

19. Domin kuwa, Ɗan Allah, Yesu Almasihu, wanda ni, da Sila, da Timoti muka yi muku wa'azi, ai, ba shiririta a game da shi, har kullum a kan gaskiya yake.

20. Domin dukan alkawaran Allah cikarsu a gare shi take, ta wurinsa ne kuma muke faɗar “Amin”, domin a ɗaukaka Allah.

21. Domin kuwa, Allah shi ne mai tabbatar da mu da ku gaba ɗaya ga Almasihu, shi ne wanda ya shafe mu kuma.

22. Ya buga mana hatiminsa cewa mu nasa ne, ya kuma yi mana baiwa da Ruhunsa a zukatanmu, domin tabbatar da abin da zai yi a nan gaba.

23. Labudda, Allah shi ne mashaidina a kan cewa, musamman don sawwaƙe muku ne, na fāsa zuwa Koranti.

24. Ba cewa muna nuna muku iko a kan bangaskiyarku ba ne, a'a, sai dai muna aiki tare ne, domin ku yi farin ciki, domin a game da bangaskiyarmu kam, kuna tsaye kankan.

Karanta cikakken babi 2 Kor 1