Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

2 Kor 1:1-11 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. Daga Bulus, manzon Almasihu Yesu da yardar Allah, da kuma ɗan'uwanmu Timoti, zuwa ga ikkilisiyar Allah da take a Koranti, tare da dukan tsarkaka na duk ƙasar Akaya.

2. Alheri da salama na Allah Ubanmu, da na Ubangiji Yesu Almasihu su tabbata a gare ku.

3. Godiya ta tabbata a gare shi, shi wanda yake Allah, da Uba na Ubangijinmu Yesu Almasihu, Uba mai yawan jinƙai, Allah na dukan ta'aziyya,

4. shi da yake yi mana ta'aziyya a dukan wahalarmu, domin mu kuma mu iya ta'azantar da masu shan kowace irin wahala, da ta'aziyyar nan da mu ma muka samu a gun Allah.

5. Domin kuwa kamar yadda muke shan wuya ƙwarai, irin wadda Almasihu ya sha, haka kuma ake yi mana ta'aziyya ƙwarai, ta wurin Almasihu.

6. Ko ana wahalshe mu ma, ai, saboda ta'azantuwarku ce, da kuma lafiyarku. Ko ana ta'azantar da mu, ai, saboda ta'azantuwarku ce, wadda take sa ku, ku jure wa irin wuyan nan, da muke sha.

7. Sa zuciyarmu a kanku ƙaƙƙarfa ce, domin mun sani, kamar yadda kuka yi tarayya da mu a cikin shan wuya, haka kuma, za ku yi tarayya a cikin ta'aziyyar.

8. 'Yan'uwa, ba ma so ku jahilta da wahalar da muka sha a ƙasar Asiya, domin kuwa mun ji jiki ƙwarai da gaske, har abin ya fi ƙarfinmu, har ma muka fid da tsammanin rayuwa.

9. Har ma muka ji kamar hukuncin kisa aka yi mana, wannan kuwa don kada mu dogara ga kanmu ne, sai dai ga Allah, mai ta da matattu.

10. Shi ne ya kuɓutar da mu daga muguwar mutuwa a fili, zai kuwa kuɓutar da mu, ga shi kuma muke dogara yă kuɓutar da mu har ila yau.

11. Ku ma sai ku taimake mu da addu'a, domin mutane da yawa su gode wa Allah, ta dalilinmu, saboda albarkar da aka yi mana, ta amsa addu'o'i masu yawa.

Karanta cikakken babi 2 Kor 1