Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

2 Bit 2:11-21 Littafi Mai Tsarki (HAU)

11. Amma kuwa mala'iku, ko da yake sun fi su ƙarfi da iko, duk da haka, ba su ɗora musu laifi da zage-zage a gaban Ubangiji.

12. Amma waɗannan mutane, kamar daddobi marasa hankali suke, masu bin abin da jikinsu ya ba su kawai, waɗanda aka haifa, don a kama a kashe, har suna kushen abubuwan da ba su fahinta ba, lalle kuwa za su hallaka a sanadin ɓacin nan nasu,

13. suna shan sakamakon muguntarsu. Sun ɗauka a kan jin daɗi ne a yi annashuwa da rana kata. Sun baƙanta, sun zama abin kunya. Sun dulmuya ga ciye-ciye da shaye-shaye, suna ta nishaɗi a cikinku.

14. Jarabar zina take a gare su, ba sa ƙoshi da yin zunubi. Suna yaudarar marasa kintsuwa. Sun ƙware da ƙwaɗayi. La'anannun iri!

15. Sun yar da miƙaƙƙiyar hanya, sun bauɗe, sun bi hanyar Bal'amu ɗan Beyor, wanda ya cika son samu ta hanyar mugunta.

16. Amma an tsawata masa a kan laifinsa, har dabba marar baki ma ta yi magana kamar mutum, ta kwaɓi haukan annabin nan.

17. Mutanen nan kamar mabubbugen ruwa wadanda suka kafe, ƙasashi ne da iska take kaɗawa. Su ne aka tanada wa matsanancin duhu.

18. Ta surutai barkatai marasa kan gado na ruba, da halinsu na fasikanci sukan shammaci waɗanda da ƙyar suke kuɓucewa daga masu zaman saɓo,

19. suna yi musu alkawarin 'yanci, ga shi kuwa, su da kansu bayin zamba ne. Don mutum bawa ne na duk abin da ya rinjaye shi.

20. In kuwa bayan da suka tsere wa ƙazantar duniyar albarkacin sanin Ubangijinmu, Mai Cetonmu Yesu Almasihu, suka kuma sāke sarƙafewa a ciki, har aka rinjaye su, ƙarshen zamansu ya fi na fari lalacewa ke nan.

21. Da ba su taɓa sanin hanyar adalci tun da fari ba, da ya fiye musu, bayan sun san ta, sa'an nan su juya ga barin umarnin nan mai tsarki.

Karanta cikakken babi 2 Bit 2