Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

1 Yah 2:18-29 Littafi Mai Tsarki (HAU)

18. Ya ku 'yan yarana, zamanin ƙarshe ne fa. Kamar yadda kuka ji, magabcin Almasihu yana zuwa, ko a yanzu ma, magabtan Almasihu da yawa sun zo. Ta haka muka sani zamanin ƙarshe ne.

19. Sun dai fita daga cikinmu, amma dā ma can ba namu ba ne. Don in da namu ne, da har yanzu suna tare da mu. Amma sun fita ne domin a bayyana dukansu ba namu a ciki.

20. Ku kam, Mai Tsarkin nan ya shafe ku, dukanku kuma kun san gaskiya.

21. Ina rubuto muku, ba don ba ku san gaskiya ba ne, a'a, sai domin kun san ta, kun kuma sani gaskiya ba ta haifar ƙarya.

22. Wane ne maƙaryacin nan, in ba wanda ya mūsa Yesu shi ne Almasihu ba? Irin wannan shi ne magabcin Almasihu, shi wanda yake ƙin Uban da Ɗan.

23. Ba mai ƙin Ɗan ya sami Uban. Kowa ya bayyana yarda ga Ɗan, ya sami Uban ke nan.

24. Ku kam, abin da kuka ji tun da farko, sai ya zauna a zuciyarku. In abin da kuka ji tun farko ya zauna a zuciyarku, ku ma sai ku zauna cikin Ɗan, da kuma Uban.

25. Wannan shi ne alkawarin da ya yi mana, wato, rai madawwami.

26. Ina rubuto muku wannan ne a kan waɗanda suke ƙoƙarin ɓad da ku.

27. Ku kam, shafar nan da kuka samu daga Ruhu Mai Tsarki tā tabbata a zuciyarku, ba sai wani ya koya muku ba. Amma kamar yadda shafar nan tasa take koya muku kome, ita kuwa gaskiya ce ba ƙarya ba, yadda dai ta koya muku, to, sai ku zauna a cikinsa.

28. To a yanzu, ya ku 'ya'yana ƙanana, sai ku zauna cikinsa, domin sa'ad da ya bayyana, mu kasance da amincewa, kada kunya ta rufe mu a gabansa a ranar komowarsa.

29. Da yake kun san shi mai adalci ne, ku dai tabbata duk mai aikata adalci haifaffensa ne.

Karanta cikakken babi 1 Yah 2