Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

1 Yah 1:6-10 Littafi Mai Tsarki (HAU)

6. In mun ce muna tarayya da shi, alhali kuwa muna zaune a duhu, mun yi ƙarya ke nan, ba ma aikata gaskiya.

7. In kuwa muna zaune a haske, kamar yadda shi yake cikin haske, muna tarayya da juna ke nan, jinin Yesu Ɗansa kuma yana tsarkake mu daga dukkan zunubi.

8. In mun ce ba mu da zunubi, ruɗin kanmu muke yi, gaskiya kuwa ba ta tare da mu.

9. In kuwa muka bayyana zunubanmu, to, shi mai alkawari ne, mai adalci kuma, zai kuwa gafarta mana zunubanmu, ya tsarkake mu daga dukkan rashin adalci.

10. In mun ce ba mu yi zunubi ba, mun ƙaryata shi ke nan. Maganarsa kuma ba ta tare da mu.

Karanta cikakken babi 1 Yah 1