Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

1 Tim 6:15-21 Littafi Mai Tsarki (HAU)

15. wannan kuwa makaɗaicin mamallaki, abin yabo, Sarkin sarakuna. Ubangijin iyayengiji zai bayyana shi a lokacinsa.

16. Shi ne kaɗai marar mutuwa, yake kuma zaune a cikin hasken da ba ya kusatuwa. Shi kuwa ba mutumin da ya taɓa ganinsa, ko kuwa zai iya ganinsa. Girma da madawwamin mulki su tabbata a gare shi. Amin, amin.

17. Masu dukiyar duniyar nan kuwa ka gargaɗe su kada su nuna alfarma, kada kuwa su dogara da dukiya marar tabbata, sai dai ga Allah, wanda yake ba mu kome a yalwace don mu ji daɗinsa.

18. Sai dai su yi nagarta da bijinta a wajen aiki nagari, su kasance masu hannu sake, suna alheri.

19. Ta haka suke kafa wa kansu kyakkyawan tushe don nan gaba, domin su riƙi rai wanda yake na hakika.

20. Ya Timoti, ka kiyaye abin da aka ba ka amana. Ka yi nesa da masu maganganun sāɓo na banza da wofi, da yawan musu da ake ƙarya, ake ce da shi ilimi.

21. Waɗansu kuwa, a garin taƙama, da haka har sun kauce wa bangaskiya.Alheri yă tabbata a gare ku.

Karanta cikakken babi 1 Tim 6