Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

1 Tim 5:14-19 Littafi Mai Tsarki (HAU)

14. Saboda haka, ina so gwauraye masu ƙuruciya waɗanda mazansu suka mutu su yi aure, su haifu, su tafiyar da al'amuran gida, kada su ba magabci hanyar zarginmu.

15. Gama waɗansu ma har sun bauɗe, sun bi Shaiɗan.

16. Duk mace mai bi, da take da dangi gwauraye mata, sai ta taimake su, kada a nauwaita wa ikkilisiya, don ikkilisiyar ta samu ta taimaki gwauraye marasa mataimaka.

17. Dattawan ikkilisiya da suke a riƙe da al'amura sosai, a girmama su ninkin ba ninkin, tun ba ma waɗanda suke fama da yin wa'azi da koyarwa ba.

18. Domin Nassi ya ce, “Kada ka sa wa takarkari takunkumi sa'ad da yake sussuka.” Ya kuma ce, “Ma'aikaci ya cancanci ladarsa.”

19. Kada ka yarda in an kawo ƙarar wani dattijon ikkilisiya, sai dai da shaidu biyu ko uku.

Karanta cikakken babi 1 Tim 5