Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

1 Tim 5:1-7 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. Kada ka tsauta wa dattijo, sai dai ka roƙe shi kamar mahaifinka. Samari kuma ka ɗauke su kamar 'yan'uwanka,

2. tsofaffi mata kuma kamar uwayenka, 'yan mata kuwa kamar 'yan'uwanka, da matuƙar tsarkaka.

3. Ka girmama gwauraye mata, waɗanda ba sa da mataimaka.

4. In wata gwauruwa tana da 'ya'ya ko jikoki, sai su koya, ya wajaba su fara nuna wa danginsu bautar Allah da suke yi, su kuma sāka wa iyayensu da alheri. Wannan abin karɓa ne a gun Allah.

5. Gwauruwa marar mataimaki kuwa, mai zaman kaɗaici, ta dogara ga Allah ke nan, tana nacewa ga roƙon Allah, tana addu'a dare da rana.

6. Amma wadda take zaman annashuwa kuwa, kamar matacciya take, ko da tana a raye.

7. Ka umarce su a game da waɗannan abubuwa, don su kasance marasa abin zargi.

Karanta cikakken babi 1 Tim 5