Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

1 Tim 4:11-16 Littafi Mai Tsarki (HAU)

11. Ka yi umarni da waɗannan abubuwa, ka kuma koyar da su.

12. Kada ka yarda kowa yă raina ƙuruciyarka, sai dai ka zama gurbi ga masu ba da gaskiya ta wurin magana, da hali, da ƙauna, da bangaskiya, da kuma tsarkaka.

13. Kafin in zo, ka lazamci karanta wa mutane Littattafai, da yin gargaɗi, da kuma koyarwa.

14. Kada ka shagala da baiwar da aka yi maka, wadda aka ba ka ta wurin annabci, sa'ad da dattawan ikkilisiya suka ɗora maka hannu.

15. Ka himmantu ga waɗannan abubuwa, ka kuma lazamce su ƙwarai, don kowa yă ga ci gaban da kake yi.

16. Ka kula da kanka da kuma koyarwarka. Ka nace da haka, domin ta yin haka za ka ceci kanka da masu sauraronka.

Karanta cikakken babi 1 Tim 4