Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

1 Tim 1:14-20 Littafi Mai Tsarki (HAU)

14. Alherin Ubangijinmu kuma ya kwararo mini ƙwarai da gaske, a game da bangaskiya, da kuma ƙaunar da take ga Almasihu Yesu.

15. Maganar nan tabbatacciya ce, ta kuma cancanci a karɓe ta ɗungum cewa, “Almasihu Yesu ya shigo duniya ne domin ceton masu zunubi,” ni ne kuwa babbansu.

16. Duk da haka an yi mini jinƙai musamman, don ta kaina, ni babbansu, Yesu Almasihu yă nuna cikakken haƙurinsa, in zama gurbi ga waɗanda a nan gaba za su gaskata da shi su sami rai madawwami.

17. Girma da ɗaukaka su tabbata ga Sarkin zamanai, marar mutuwa, marar ganuwa, Allah Makaɗaici, har abada abadin. Amin, amin.

18. Na danƙa maka wannan umarni, ya ɗana Timoti, bisa ga annabce-annabcen da dā aka faɗa a kanka, domin ka ƙarfafu ta wurinsu, ka yi yaƙi mai kyau,

19. kana riƙe da bangaskiya da lamiri mai kyau. Gama waɗansu mutane, saboda ƙin kasa kunne ga lamirinsu, suka lalatar da bangaskiyarsu.

20. Cikinsu har da Himinayas da Askandari, waɗanda na miƙa wa Shaiɗan, don su horo su bar yin sāɓo.

Karanta cikakken babi 1 Tim 1