Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

1 Tas 5:4-9 Littafi Mai Tsarki (HAU)

4. Amma, ai, ba a cikin duhu kuke ba, 'yan'uwa, har da ranar nan za ta mamaye ku kamar ɓarawo.

5. Domin duk mutanen haske kuke, na rana kuma. Mu ba na dare ko na duhu ba ne.

6. Ashe, saboda haka kada mu yi barci yadda waɗansu suke yi, sai dai mu zauna a faɗake, da natsuwa.

7. Don masu barci da daddare suke barci, masu sha su bugu ma da daddare suke sha su bugu.

8. Amma da yake mu na rana ne, sai mu natsu, muna saye da sulken bangaskiya da ƙauna, muna begen samun ceto, shi ne kuma kwalkwakinmu.

9. Allah bai ƙaddara mu ga fushinsa ba, sai dai ga samun ceto ta wurin Ubangijinmu Yesu Almasihu,

Karanta cikakken babi 1 Tas 5