Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

1 Tas 4:16-18 Littafi Mai Tsarki (HAU)

16. domin Ubangiji kansa ma zai sauko daga Sama, da kira mai ƙarfi, da muryar babban mala'ika, da kuma busar ƙahon Allah. Waɗanda suka mutu suna na Almasihu, su ne za fara tashi,

17. sa'an nan sai mu da muka wanzu, muke a raye, za a ɗauke mu tare da su ta cikin gajimare, mu sadu da Ubangiji a sararin sama, sai kuma kullum mu kasance tare da Ubangiji.

18. Saboda haka, sai ku yi wa juna ta'aziyya da wannan magana.

Karanta cikakken babi 1 Tas 4