Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

1 Tas 4:1-7 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. Daga ƙarshe kuma 'yan'uwa, muna roƙonku, muna kuma yi muku gargaɗi saboda Ubangiji Yesu, cewa kamar yadda kuka koya a wurinmu, irin zaman da ya dace da ku, ku faranta wa Allah rai, kamar yadda yanzu ma kuke yi, to, sai ku ƙara yin haka ƙwarai da gaske,

2. domin kun san umarnin nan da muka yi muku da iznin Ubangiji Yesu.

3. Gama wannan shi ne nufin Allah, wato ku yi zaman tsarki, ku guje wa fasikanci,

4. kowannenku kuma ya san yadda zai auro matarsa da tsarki da mutunci,

5. ba ta muguwar sha'awa ba, yadda al'ummai suke yi, waɗanda ba su san Allah ba.

6. A cikin wannan al'amari kuwa kada kowa ya keta haddi, har ya cuci ɗan'uwansa, domin Ubangiji mai sakamako ne a kan dukkan waɗannan abubuwa, kamar yadda muka gargaɗe ku, muka tabbatar muku tun da wuri.

7. Ai, ba a zaman ƙazanta ne Allah ya kira mu ba, amma ga zaman tsarki ne.

Karanta cikakken babi 1 Tas 4