Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

1 Tas 3:7-13 Littafi Mai Tsarki (HAU)

7. Saboda haka 'yan'uwa, cikin dukan wahala da ƙuncin da muka sha, an sanyaya mana zuciya a game da ku, albarkacin bangaskiyarku.

8. A yanzu kam a raye muke, in dai kun tsaya ga Ubangiji.

9. Wace irin godiya za mu yi wa Allah saboda ku, a kan matuƙar farin cikin da muke yi a gaban Allahnmu ta dalilinku!

10. Dare da rana muna nacin addu'a ƙwarai mu sami ganinku ido da ido, mu kuma cikasa abin da ya gaza wajen bangaskiyarku.

11. Muna fata dai Allahnmu, ubanmu, shi kansa, da kuma Ubangijinmu Yesu, ya kai mu gare ku.

12. Ku kuma, Ubangiji ya sa ku ƙaru, ku kuma yalwata da ƙaunar juna da dukan mutane, kamar yadda muke yi muku,

13. har ya tsai da zukatanku ku zama marasa abin zargi cikin tsarki a gaban Allahnmu, Ubanmu, a ranar komowar Ubangijinmu Yesu, tare da dukan tsarkakansa.

Karanta cikakken babi 1 Tas 3