Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

1 Kor 9:8-14 Littafi Mai Tsarki (HAU)

8. Wato, ina faɗar haka bisa ga ra'ayin mutum kawai ne? Ba haka ma Attaura ta faɗa ba?

9. Ai, haka yake a rubuce a Shari'ar Musa cewa, “Kada ka sa wa takarkari takunkumi a sa'ad da yake sussuka.” Da shanu ne kawai Allah yake kula?

10. Ba saboda mu musamman yake magana ba? Hakika saboda mu ne aka rubuta. Ai, ya kamata mai noma yă yi noma da sa zuciya, mai sussuka kuma yă yi sussuka da sa zuciya ga samun rabo daga amfanin gonar.

11. Da yake mun shuka iri na ruhu a zuciyarku, to, wani ƙasaitaccen abu ne, in mun mori amfaninku irin na duniya?

12. Da yake waɗansu sun mori halaliyarsu a game da ku, ashe ba mu muka fi cancanta ba?Duk da haka ba mu mori wannan halaliya ba, sai dai muna jure wa kome, don ta koƙaƙa kada mu hana bisharar Almasihu yaɗuwa.

13. Ashe, ba ku sani ba, masu hidima a Haikali daga nan suke samun abincinsu? Masu hidimar bagadi kuma, a nan suke samun rabo daga hadayar da aka yanka?

14. Haka nan kuma Ubangiji ya yi umarni, cewa, ya kamata masu sanar da bishara, a cishe su albarkacin bishara.

Karanta cikakken babi 1 Kor 9