Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

1 Kor 7:1-9 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. To, a yanzu, a game da abin da kuka rubuto, yana da kyau mutum ya zauna ba aure.

2. Amma don gudun fasikanci sai kowane mutum ya kasance da matarsa, kowace mace kuma da mijinta.

3. Miji yă ba matarsa hakkinta na aure, haka kuma matar ga mijinta.

4. Matar kuwa ba ta da iko da jikinta, sai dai mijin, haka kuma mijin ba shi da iko da jikinsa, sai dai matar.

5. Kada ɗayanku yă ƙaurace wa ɗaya, sai ko da yardar juna zuwa wani ɗan lokaci kaza, don ku himmantu ga addu'a, sa'an nan ku sāke haɗuwa, kada Shaiɗan yă zuga ku ta wajen rashin kamewa.

6. Na fadi wannan ne bisa ga shawara, ba bisa ga umarni ba.

7. Da ma a ce kowa kamar ni yake mana! Sai dai kowa da irin baiwar da Allah ya yi masa, wani iri kaza, wani kuma iri kaza.

8. Abin da na gani ga waɗanda ba su yi aure ba, da kuma mata gwauraye, ya kyautu a gare su su zauna ba aure kamar yadda nake.

9. In kuwa ba za su iya kamewa ba, to, sai su yi aure. Ai, gwamma dai a yi aure da sha'awa ta ci rai.

Karanta cikakken babi 1 Kor 7