Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

1 Kor 6:1-10 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. In waninku yana da wata ƙara a game da ɗan'uwansa, ashe, zai yi ƙurun kai maganar a gaban marasa adalci, ba a gaban tsarkaka ba?

2. Ashe, ba ku sani ba, tsarkaka ne za su yi wa duniya shari'a? In kuwa ku ne za ku yi wa duniya shari'a, ashe, ba za ku iya shari'ar ƙananan al'amura ba?

3. Ba ku sani ba, za mu yi wa mala'iku shari'a, balle al'amuran da suka shafi zaman duniyar nan?

4. In kuwa kuna da irin waɗannan ƙararraki, don me kuma kuke kai su gaban waɗanda su ba kome ba ne, a game da Ikkilisiya?

5. Na faɗi wannan ne don ku kunyata. Ashe, wato, ba ko mutum ɗaya mai hikima a cikinku, da zai iya sasanta tsakanin 'yan'uwa?

6. Amma ɗan'uwa yakan kai ƙarar ɗan'uwa, gaban marasa ba da gaskiya kuma?

7. Ku yi ƙarar juna ma, ai, hasara ce a gare ku. Ba gara ku haƙura a cuce ku ba? Ku kuma haƙura a zambace ku?

8. Amma, ga shi, ku da kanku kuna cuta, kuna zamba, har ma 'yan'uwanku kuke yi wa!

9. Ashe, ba ku sani ba, marasa adalci ba za su sami gādo a cikin Mulkin Allah ba? Kada fa a yaudare ku! Ba fasikai, ko matsafa, ko mazinata, ko masu luɗu da maɗugo,

10. ko ɓarayi, ko makwaɗaita, ko mashaya, ko masu zage-zage, ko mazambata, da za su sami gādo a cikin Mulkin Allah.

Karanta cikakken babi 1 Kor 6