Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

1 Kor 4:8-21 Littafi Mai Tsarki (HAU)

8. Mhm, wato, har kun riga kun yi hamdala! Har kun wadata! Har ma kun yi sarauta ba tare da mu ba ma! Da ma a ce kun yi mulki mana, har mu ma mu yi tare da ku!

9. Don a ganina, Allah ya bayyana mu, mu manzanni, koma bayan duka ne, kamar waɗanda mutuwa yake jewa a kansu, don mun zama abin nuni ga duniya, da mala'iku duk da mutane.

10. An ɗauke mu marasa azanci saboda Almasihu, wato, ku kuwa masu azanci cikin Almasihu! Wato, mu raunana ne, ku kuwa ƙarfafa! Ku kam, ana ganinku da martaba, mu kuwa a wulakance!

11. Har a yanzu haka, yunwa muke ji, da ƙishirwa, muna huntanci, ana bugunmu, kuma yawo muke yi haka, ba mu da gida.

12. Guminmu muke ci. In an zage mu, mukan sa albarka. In an tsananta mana, mukan daure.

13. In an ci mutuncinmu, mukan ba da haƙuri. Mun zama, har a yanzu ma, mu ne kamar jujin duniya, abin ƙyamar kowa.

14. Ba don in kunyata ku na rubuta wannan ba, sai dai don in gargaɗe ku a kan cewa, ku 'ya'yana ne, ƙaunatattu.

15. Ko da kuna da malamai masu ɗumbun yawa, amma ba ku da ubanni da yawa, don ni ne ubanku a cikin Almasihu ta wurin bishara.

16. Don haka, ina roƙon ku, ku yi koyi da ni.

17. Saboda haka, na aika muku da Timoti, wanda yake shi ne ɗana ƙaunatacce, amintacce kuma a cikin Ubangiji, zai kuwa tuna muku da ka'idodina na bin Almasihu, kamar yadda nake koyarwa a ko'ina, a kowace ikkilisiya.

18. Waɗansu har suna ɗaga kai, kamar ba zan zo wurinku ba.

19. Amma kuwa zan zo gare ku ba da daɗewa ba, in Ubangiji ya yarda, zan kuma bincika, in ga ƙarfin mutane masu ɗaga kan nan, ba maganganunsu ba.

20. Domin Mulkin Allah ba ga maganar baka yake ba, sai dai ga ƙarfi.

21. To, me kuka zaɓa, in zo muku da sanda, ko kuwa da fuskar ƙauna da lumana?

Karanta cikakken babi 1 Kor 4