Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

1 Kor 3:2-5 Littafi Mai Tsarki (HAU)

2. Nono ne na shayar da ku, ba abinci mai tauri na ba ku ba, don ba ku isa ci ba a lokacin, ko a yanzu ma ba ku isa ba,

3. don har a yanzu ku masu halin mutuntaka ne. Muddin akwai kishi da jayayya a tsakaninku, ashe, ku ba masu halin mutuntaka ba ne, kuna kuma aikata halin mutuntaka?

4. Don in wani ya ce, “Ni na Bulus ne,” wani kuma ya ce, “Ni na Afolos ne,” ashe, ba aikata halin mutuntaka kuke yi ba?

5. To, wane ne Afolos? wane ne Bulus kuma? Ashe, ba bayi ne kawai ba, waÉ—anda kuka ba da gaskiya ta wurinsu, ko wannensu kuwa gwargwadon abin da Ubangiji ya ba shi?

Karanta cikakken babi 1 Kor 3