Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

1 Kor 3:17-23 Littafi Mai Tsarki (HAU)

17. In wani ya ɓāta Haikalin Allah, Allah zai ɓāta shi. Gama Haikalin Allah tsattsarka ne, ku kanku Haikalinsa ne.

18. Kada kowa yă ruɗi kansa. In waninku ya zaci shi mai hikima ne, yadda duniya ta ɗauki hikima, sai yă mai da kansa marar hikima, domin ya sami zama mai hikima.

19. Gama hikimar duniyar nan wauta ce a gun Allah, domin a rubuce yake, “Yakan kama masu hikima da makircinsu.”

20. Har wa yau, “Ubangiji ya san tunanin masu hikima banza ne.”

21. Saboda haka kada kowa yă yi fariya da 'yan adam. Don kuwa kome naku ne,

22. ko Bulus, ko Afolos, ko Kefas, ko duniya, ko rai, ko mutuwa, ko abubuwan yanzu, ko da na gaba, ai, duk naku ne.

23. Ku kuwa na Almasihu ne, Almasihu kuma na Allah ne.

Karanta cikakken babi 1 Kor 3