Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

1 Kor 2:11-16 Littafi Mai Tsarki (HAU)

11. Wane ne a cikin mutane ya san tunanin wani mutum, in ba ruhun shi mutumin ba? Haka kuma ba wanda ya san tunanin Allah, sai dai Ruhun Allah.

12. Mu kuwa ba ruhun duniya muka samu ba, sai dai Ruhu wanda yake daga wurin Allah, domin mu fahimci abubuwan da Allah ya yi mana baiwa hannu sake.

13. Su ne kuwa muke sanarwa ta maganar da ba hikimar ɗan adam ce ta koyar ba, sai dai wadda Ruhu ya koyar, muna bayyana al'amura masu ruhu ga waɗanda suke na ruhu.

14. Mutumin da ba shi da Ruhu yakan ƙi yin na'am da al'amuran Ruhun Allah, don wauta ne a gare shi, ba kuwa zai iya fahimtarsu ba, domin ta wurin ruhu ne ake rarrabewa da su.

15. Mutumin da yake na ruhu kuwa yakan rarrabe da kome, shi kansa kuma ba mai jarraba shi.

16. “Wa ya taɓa sanin tunanin Ubangiji, har da zai koya masa?” Mu kuwa tunaninmu na Almasihu ne.

Karanta cikakken babi 1 Kor 2