Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

1 Kor 15:48-55 Littafi Mai Tsarki (HAU)

48. Kamar yadda shi na turɓayar nan yake, haka kuma waɗanda suke na turɓaya suke. Kamar yadda shi na Saman nan yake, haka kuma waɗanda suke na Sama suke.

49. Kamar yadda muka ɗauki siffar na turɓayar nan, haka kuma za mu ɗauki siffar na Saman nan.

50. Ina dai gaya muku wannan 'yan'uwa, ba shi yiwuwa jiki mai tsoka da jini ya sami gādo a Mulkin Allah, haka kuma mai ruɓa ba ya gādon marar ruɓa.

51. Ga shi, zan sanar da ku wani asiri! Ba dukanmu ne za mu yi barci ba, amma dukanmu za a sauya kamanninmu,

52. farat ɗaya da ƙyiftawar ido, da jin busar ƙaho na ƙarshe, domin za a busa ƙaho, za a kuma ta da matattu da halin rashin ruɓa, za a kuma sauya kamanninmu.

53. Domin lalle ne, marar ruɓa ya maye mai ruɓar nan, marar mutuwa kuma ya maye mai mutuwar nan.

54. Sa'ad da kuma marar ruɓa ya maye mai ruɓar nan, marar mutuwa kuma ya maye mai mutuwar nan, a sa'an nan ne fa maganar nan da take a rubuce za a cika ta, cewa,“An shafe mutuwa da aka ci nasararta.”

55. “Ke mutuwa, ina nasararki?Ke mutuwa, ina ƙarinki?”

Karanta cikakken babi 1 Kor 15