Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

1 Kor 15:21-34 Littafi Mai Tsarki (HAU)

21. Tun da yake mutuwa ta wurin mutum ta faru, haka kuma tashin matattu ta wurin Mutum yake.

22. Kamar yadda duk ake mutuwa saboda Adamu, haka duk za a rayar da su saboda Almasihu.

23. Amma kowanne bi da bi, Almasihu ne nunan fari, sa'an nan a ranar komowarsa, waɗanda suke na Almasihu.

24. Sa'an nan sai ƙarshen, sa'ad da zai mayar wa Allah Uba mulki, bayan ya shafe dukkan sarauta da mulki da iko.

25. Domin kuwa lalle ne ya yi mulki, har ya take dukkan maƙiyansa.

26. Magabciyar ƙarshe da za a shafe, ita ce mutuwa.

27. “Gama Allah ya sarayar da kome a ƙarƙashin ikonsa.” Amma da aka ce, “An sarayar da kome karƙashin ikonsa” a fili yake shi wannan da ya sarayar da kome a ƙarƙashin ikonsa ɗin, a keɓe yake.

28. Sa'ad da kuma aka sarayar da kome a ƙarƙashin ikonsa ɗin, sa'an nan ne Ɗan da kansa shi ma zai sarayar da kansa ga wannan da ya sarayar da kome a ƙarƙashin ikonsa, domin Allah yă tabbata shi ne kome da kome.

29. In ba haka ba, mene ne nufin waɗanda ake yi wa baftisma saboda matattu? In ba a ta da matattu sam, don me ake yi wa waɗansu baftisma saboda su?

30. Don me kuma nake a cikin hatsari a kowane lokaci?

31. Na hakikance 'yan'uwa, saboda taƙama da ku da nake yi a cikin Almasihu Yesu Ubangijinmu, a kowace rana sai na sallama raina ga mutuwa!

32. Idan bisa ga ra'ayin mutum ne, na yi kokawa da namomin jeji a Afisa, mece ce ribata in dai har ba a ta da matattu? “Ba sai mu yi ta ci da sha ba, da yake gobe za mu mutu?”

33. Kada fa a yaudare ku! “Zama da mugaye yakan ɓata halayen kirki.”

34. Ku farka daga magagi, ku kama aikin adalci, ku daina yin zunubi. Waɗansu kam, ba su da sanin Allah. Na faɗi wannan ne don ku kunyata.

Karanta cikakken babi 1 Kor 15