Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

1 Kor 15:15-24 Littafi Mai Tsarki (HAU)

15. Sai ma ya zamana mun yi wa Allah shaidar zur ke nan, domin mun shaida Allah, cewa ya ta da Almasihu, wanda kuwa bai tasar ba, in da gaskiya ne ba a ta da matattu.

16. Don kuwa in ba a ta da matattu, ashe, Almasihu ma ba a ta da shi ba ke nan.

17. In kuwa ba a ta da Almasihu ba, ashe, bangaskiyarku banza ce, har yanzu kuma kuna tare da zunubanku.

18. Ashe, waɗanda suka yi barci a kan su na Almasihu, sun hallaka ke nan.

19. Da begenmu ga Almasihu domin wannan rai ne kaɗai, ai, da mun fi kowa zama abin tausayi.

20. Amma ga hakika an ta da Almasihu daga matattu, shi ne ma nunan fari na waɗanda suka yi barci.

21. Tun da yake mutuwa ta wurin mutum ta faru, haka kuma tashin matattu ta wurin Mutum yake.

22. Kamar yadda duk ake mutuwa saboda Adamu, haka duk za a rayar da su saboda Almasihu.

23. Amma kowanne bi da bi, Almasihu ne nunan fari, sa'an nan a ranar komowarsa, waɗanda suke na Almasihu.

24. Sa'an nan sai ƙarshen, sa'ad da zai mayar wa Allah Uba mulki, bayan ya shafe dukkan sarauta da mulki da iko.

Karanta cikakken babi 1 Kor 15