Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

1 Kor 14:27-40 Littafi Mai Tsarki (HAU)

27. In kuwa waɗansu za su yi magana da wani harshe, kada su fi mutum biyu, matuƙa uku, su ma kuwa bi da bi, wani kuma yă yi fassara.

28. In kuwa ba mai fassara, sai kowannensu yă yi shiru a cikin taron Ikkilisiya, yă yi wa Allah magana a zuci.

29. Masu yin annabci kuma, sai dai biyu ko uku su yi magana, saura kuwa su auna maganar.

30. In kuwa an yi wa wani wanda yake zaune wani bayani, sai na farkon nan mai magana yă yi shiru.

31. Dukanku kuna iya yin annabci da ɗaya ɗaya, har kowa yă koya, yă koma sami ƙarfafawa.

32. Annabawa suna sarrafa ruhohinsu na annabci,

33. domin Allah ba Allahn ruɗu ba ne, na salama ne.Haka yake kuwa a duk ikilisyoyin tsarkaka.

34. Sai mata su yi shiru a cikin taron ikkilisiya, don ba a ba su izinin yin magana ba, sai dai su bi, kamar dai yadda Attaura ma ta ce.

35. In akwai wani abin da suke so su sani, to, sai su tambayi mazansu a gida, don abin kunya ne mace ta yi magana a cikin taron ikkilisiya.

36. A kanku ne maganar Allah ta fara, ko kuwa a gare ku kaɗai ta isa?

37. In wani yana zato shi annabi ne, ko kuwa mai wata baiwa ta ruhu, to, sai yă fahimta, abin nan da nake rubuto muku umarni ne na Ubangiji.

38. In kuwa wani ya ƙi kula da wannan, shi ma sai a ƙi kula da shi.

39. Saboda haka, 'yan'uwa, sai ku himmantu ga samun baiwar yin annabci, kada kuma ku hana yin magana da waɗansu harsuna.

40. Sai dai a yi kome ta hanyar da ta dace, a shirye kuma.

Karanta cikakken babi 1 Kor 14