Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

1 Kor 12:6-14 Littafi Mai Tsarki (HAU)

6. Akwai kuma aiki iri iri, amma Allah ɗaya yake iza kowa ga yin kowannensu.

7. An yi wa kowanne baiwa da wani buɗi na Ruhu, don kyautata wa duka.

8. Wani an yi masa baiwa da koyar da hikima ta wurin Ruhu, wani kuma da koyar da sani ta wurin wannan Ruhu.

9. Wani kuwa an yi masa baiwa da bangaskiya ta wurin Ruhun nan, wani kuma baiwar warkarwa ta wurin Ruhun nan,

10. wani kuma yin mu'ujizai, wani kuma annabci, wani kuma baiwar rarrabe ruhu da aljani, wani kuma iya harshe iri iri, wani kuma fassara harsuna.

11. Dukan waɗannan Ruhu ɗaya ne da yake iza su, yake kuma rarraba wa ko wannensu yadda ya nufa.

12. Wato, kamar yadda jiki yake guda, yake kuma da gaɓoɓi da yawa su gaɓoɓin kuwa ko da yake suna da yawa, jiki guda ne, to, haka ga Almasihu.

13. Dukanmu an yi mana baftisma ta wurin Ruhu guda, mu zama jiki guda, Yahudawa ko al'ummai, bayi ko 'ya'ya, dukanmu kuwa an shayar da mu Ruhu guda.

14. Jiki ba gaba ɗaya ba ne, gaɓoɓi ne da yawa.

Karanta cikakken babi 1 Kor 12