Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

1 Kor 12:1-10 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. A yanzu kuma 'yan'uwa, a game da baye-baye na ruhu, ba na so ku rasa sani.

2. Kun sani fa a sa'ad da kuke bin al'ummai, an juyar da ku ga bin gumakan nan marasa baki yadda aka ga dama.

3. Don haka nake sanar da ku, cewa ba mai magana ta wurin ikon Ruhun Allah sa'an nan ya ce, “Yesu la'ananne ne!” Haka kuma ba mai iya cewa, “Yesu Ubangiji ne,” sai ta wurin ikon Ruhu Mai Tsarki.

4. To, akwai baiwa iri iri, amma Ruhu ɗaya ne.

5. Akwai fanni iri iri na ibada, amma Ubangiji ɗaya ne.

6. Akwai kuma aiki iri iri, amma Allah ɗaya yake iza kowa ga yin kowannensu.

7. An yi wa kowanne baiwa da wani buɗi na Ruhu, don kyautata wa duka.

8. Wani an yi masa baiwa da koyar da hikima ta wurin Ruhu, wani kuma da koyar da sani ta wurin wannan Ruhu.

9. Wani kuwa an yi masa baiwa da bangaskiya ta wurin Ruhun nan, wani kuma baiwar warkarwa ta wurin Ruhun nan,

10. wani kuma yin mu'ujizai, wani kuma annabci, wani kuma baiwar rarrabe ruhu da aljani, wani kuma iya harshe iri iri, wani kuma fassara harsuna.

Karanta cikakken babi 1 Kor 12