Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

1 Kor 10:16-25 Littafi Mai Tsarki (HAU)

16. Ƙoƙon nan na yin godiya, wanda muke gode wa Allah saboda shi, ashe, ba tarayya ne ga jinin Almasihu ba? Gurasar nan da muke gutsuttsurawa kuma, ashe, ba tarayya ce ga jikin Almasihu ba?

17. Da yake gurasar nan ɗaya ce, ashe kuwa, mu da muke da yawa jiki ɗaya ne, gama mu duk gurasa ɗaya muke ci.

18. Ku dubi ɗabi'ar Isra'ila. Ashe, waɗanda suke ci daga hadayu, ba tarayya suke yi da bagadin hadaya ba?

19. Me nake nufi ke nan? Abin da aka yanka wa gumakan ne ainihin wani abu, ko kuwa gunkin ne ainihin wani abu?

20. A'a! Na nuna ne kawai cewa abin da al'ummai suke yankawa, ga aljannu suke yanka wa, ba Allah ba. Ba na fa so ku zama abokan tarayya da aljannu.

21. Ba dama ku sha a ƙoƙon Ubangiji, ku kuma sha a na aljannu. Ba dama ku ci abinci a teburin Ubangiji, ku kuma ci a na aljannu.

22. Ashe, har mā tsokani Ubangiji ya yi kishi? Mun fi shi ƙarfi ne?

23. “Dukan abubuwa halal ne,” amma ba dukan abubuwa ne masu amfani ba. “Dukan abubuwa halal ne,” amma ba dukan abubuwa ne suke ingantawa ba.

24. Kada kowa ya nemi ya kyautata wa kansa, sai dai ya kyautata wa ɗan'uwansa.

25. Ku ci kowane irin abu da ake sayarwa a mahauta, ba tare da tambaya ba saboda lamiri.

Karanta cikakken babi 1 Kor 10