Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

1 Kor 1:1-8 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. Daga Bulus, manzo kirayayye na Almasihu Yesu da yardar Allah, da kuma ɗan'uwanmu Sastanisu,

2. zuwa ga ikkilisiyar Allah da take a Koranti, wato, su waɗanda aka keɓe a cikin Almasihu Yesu, tsarkaka kirayayyu, tare da dukan waɗanda a ko'ina suke addu'a, da sunan Ubangijinmu Yesu Almasihu, Ubangijinsu da namu duka.

3. Alheri da salama na Allah Ubanmu, da na Ubangiji Yesu Almasihu su tabbata a gare ku.

4. Kullum nakan gode wa Allah dominku, saboda alherin Allah da aka yi muku baiwa ta hanyar Almasihu Yesu,

5. har ta kowace hanya aka wadata ku a cikinsa, a wajen yin magana duka da ilimi duka–

6. domin kuwa an tabbatar da shaida a kan Almasihu a cikinku.

7. Har ma ku ba kāsassu ba ne a wajen samun kowace baiwar Allah, kuna zuba ido ga bayyanar Ubangijinmu Yesu Almasihu.

8. wanda zai tabbatar da ku har ya zuwa ƙarshe, ku kasance marasa abin zargi a ranar Ubangijinmu Yesu Almasihu.

Karanta cikakken babi 1 Kor 1