Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

1 Bit 3:6-13 Littafi Mai Tsarki (HAU)

6. kamar yadda Saratu ta bi Ibrahim, tana kiransa ubangijinta. Ku kuma 'ya'yanta ne muddin kuna aiki nagari, ba kwa yarda wani abu ya tsorata ku.

7. Haka kuma, ku maza, ku yi zaman ɗa'a da matanku, kuna girmama su, da yake su ne raunana, gama ku abokan tarayya ne na Allah. Ku yi haka don kada wani abu ya hana ku yin addu'a tare.

8. Daga ƙarshe kuma dukanku ku haɗa hankulanku, ku zama masu juyayi, masu ƙaunar 'yan'uwa, masu tausayi, da kuma masu tawali'u.

9. Kada ku rama mugunta da mugunta, ko zagi da zagi, a maimakon haka, sai ku sa albarka. Domin a kan haka ne musamman aka kira ku, ku kuma gaji albarka.

10. Domin,“Duk mai so ya more wa zamansa na duniya da alheri,Sai ya kame bakinsa daga ɓarna,Ya kuma hana shi maganar yaudara.

11. Ya rabu da mugunta,ya kama nagarta,Ya himmantu ga zaman lafiya, ya kuma dimance ta.

12. Gama Ubangiji yana lura da masu aikata adalci,Yana kuma sauraron roƙonsu.Amma Ubangiji yana gāba da masu aikata mugunta.”

13. To, wa zai cuce ku in kun himmantu a kan abin da yake nagari?

Karanta cikakken babi 1 Bit 3