Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

1 Bit 3:13-22 Littafi Mai Tsarki (HAU)

13. To, wa zai cuce ku in kun himmantu a kan abin da yake nagari?

14. Amma ko da za ku sha wuya saboda aikata abin da yake daidai, ku masu albarka ne. Kada ku ji tsoronsu, kada kuma ku damu.

15. Sai dai ku girmama Almasihu a zukatanku da hakikancewa, shi Ubangiji ne. Kullum ku zauna a shirye ku ba da amsa ga duk wanda ya tambaye ku dalilin begen nan naku, amma fa da tawali'u da bangirma.

16. Ku kuma kasance da lamiri mai kyau, don in an zage ku, waɗanda suka kushe kyakkyawan halinku na bin Almasihu su kunyata.

17. Zai fi kyau a sha wuya ga yin abin da yake nagari, in haka nufin Allah ne, da a sha don yin abin da ba daidai ba.

18. Domin Almasihu ma ya mutu sau ɗaya tak ba ƙari, domin kawar da zunubanmu, mai adalci saboda marasa adalci, domin ya kai mu ga Allah. An kashe shi a jiki, amma an rayar da shi a ruhu.

19. Da ruhun ne kuma ya je ya yi wa ruhohin da suke a kurkuku shela,

20. wato, waɗanda dā ba su bi ba, sa'ad da Allah ya yi jira da haƙuri a zamanin Nuhu, a lokacin sassaƙar jirgin nan, wanda a cikinsa mutane kaɗan, wato takwas suka kuɓuta ta ruwa.

21. Baftisma kuwa, wadda ita ce kwatancin wannan, ta cece ku a yanzu, ba ta fitar da dauɗa daga jiki ba, sai dai ta wurin roƙon Allah da lamiri mai kyau, ta wurin tashin Yesu Almasihu daga matattu,

22. wanda ya tafi Sama, yake dama ga Allah kuma, mala'iku da manyan mala'iku da masu iko suna binsa.

Karanta cikakken babi 1 Bit 3