Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

1 Bit 2:9-17 Littafi Mai Tsarki (HAU)

9. Amma ku kabila ce zaɓaɓɓiya, ƙungiyar firistocin babban Sarki, tsattsarkar al'umma, jama'ar mallakar Allah, domin ku sanar da mafifitan al'amuran wannan da ya kirawo ku daga cikin duhu, kuka shiga maɗaukakin haskensa.

10. Dā ba jama'a ɗaya kuke ba, amma a yanzu, ku jama'ar Allah ce. Dā ba ku sadu da jinƙansa ba, amma a yanzu kun sadu da shi.

11. Ya ƙaunatattuna, ina roƙonku don ku baƙi ne, bare kuma, ku guje wa mugayen sha'awace-sha'awace na halin mutuntaka waɗanda suke yaƙi da zuciyarku.

12. Ku yi halin yabo a cikin al'ummai, don duk sa'ad da suke kushenku, cewa ku mugaye ne, sai su ga kyawawan ayyukanku, har su ɗaukaka Allah a ran da alheri ya sauko musu.

13. Ku yi biyayya ga kowace hukumar mutane saboda Ubangiji, ko ga sarki, domin shi ne shugaba,

14. ko kuwa ga mahukunta, domin su ne ya a'aika su hori mugaye, su kuma yabi masu kirki.

15. Domin nufin Allah ne ku toshe jahilcin marasa azanci ta yin aiki nagari.

16. Ku yi zaman 'yanci, sai dai kada ku fake a bayan 'yancin nan naku, ku yi mugunta. Amma ku yi zaman bayin Allah.

17. Ku girmama kowa, ku ƙaunaci 'yan'uwa, ku ji tsoron Allah, ku girmama sarki.

Karanta cikakken babi 1 Bit 2