Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

1 Bit 2:1-6 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. Saboda haka, sai ku yar da kowace irin ƙeta, da ha'inci, da munafunci, da hassada, da kuma kowane irin kushe.

2. Kamar jariri sabon haihuwa, ku yi marmarin shan madara marar gami mai ruhu, domin ku girma da shi, har ya kai ku ga samun ceto,

3. in dai kun ɗanɗana alherin Ubangiji.

4. Ku zo a gare shi, rayayyen dutsen nan, hakika abin ƙi ne a gun mutane, amma zaɓaɓɓe, ɗaukakakke a gun Allah.

5. Ku kuma, kamar rayayyun duwatsu, bari a gina gida mai ruhu da ku, domin ku zama tsattsarkar ƙungiyar firistoci, da nufin ku miƙa hadayu na ruhu, abin karɓa ga Allah, ta wurin Yesu Almasihu,

6. Domin a tabbace yake a Nassi cewa,“Ga shi, na sa mafificin dutsen a gini a Sihiyona, zaɓaɓɓe, ɗaukakakke,Duk mai gaskatawa da shi kuwa, ba zai kunyata ba.”

Karanta cikakken babi 1 Bit 2