Sa'an nan Ruhun Ubangiji ya sauko a kansa da iko, ya gangara zuwa Ashkelon. Ya kashe mutum talatin a can, ya kwashe ganima, ya ba waɗanda suka faɗa masa amsar ka-cici-ka-cicin riguna. Ya koma gida a husace saboda abin da ya faru.