Mutanen Mowab za su yi kuka saboda wahalar da suke sha. Dukansu za su yi kuka sa'ad da suka tuna da kyakkyawan abincin da suka riƙa ci a birnin Kir-hareset. Za a kore su har su fid da zuciya.