Sai Musa ya sassaƙa alluna biyu na dutse kamar na farko, ya tashi da sassafe, ya hau Dutsen Sina'i, kamar yadda Ubangiji ya umarce shi. Ya riƙe allunan nan biyu na dutse a hannunsa.