Za ka tsarkake ƙirji na hadaya ta kaɗawa, da cinya ta hadaya ta ɗagawa da za a kaɗa a kuma ɗaga na ragon keɓewa, wanda yake na Haruna da wanda yake na 'ya'yansa maza.