“Wannan shi ne girman bagaden bisa ga tsawon kamu. A nan kamu guda daidai yake da kamu guda da taƙi. Gindinsa kamu ɗaya ne, faɗinsa kuma kamu ɗaya, faɗin da'irarsa taƙi guda ne.