Ahaziya yana da shekara arba'in da biyu sa'ad da ya ci sarauta, ya kuwa yi mulki shekara guda a Urushalima. Sunan tsohuwarsa Ataliya jikar Omri.