Ta haka Yehu, ɗan Yehoshafat, wato jikan Nimshi, ya tayar wa Yehoram. A lokacin, Yehoram tare da dukan Isra'ila suna tsaron Ramot-gileyad, don kada Hazayel, Sarkin Suriya, ya fāɗa mata.