Shi wannan Shelomit da 'yan'uwansa suke lura da kyautai waɗanda sarki Dawuda, da shugabannin, gidajen kakanni, da shugabannin dubu dubu, da na ɗari ɗari, da shugabannin sojoji suka keɓe ga Allah.