A daidai fāɗuwar rana, duk waɗanda suke da marasa lafiya, masu cuta iri iri, suka kakkawo su wurinsa. Sai ya ɗaɗɗora wa kowannensu hannu, ya warkar da su.