Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Filib 4:1-13 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. Saboda haka ya 'yan'uwana, ƙaunatattuna, waɗanda nake bege, ku da kuke abin farin cikina da abin taƙamata kuma, ku dage ga Ubangiji, ya ku ƙaunatattuna.

2. Na gargaɗi Afodiya, na kuma gargaɗi Sintiki, su yi zaman lafiya da juna saboda su na Ubangiji ne.

3. Ya kai abokin bautata na hakika, ina roƙonka, ka taimaki matan nan, don sun yi fama tare da ni a al'amarin bishara, haka ma Kilemas da sauran abokan aikina, waɗanda sunayensu suke a rubuce a cikin Littafin Rai.

4. A kullum ku yi farin ciki da Ubangiji, har wa yau ina dai ƙara gaya muku, ku yi farin ciki.

5. Bari kowa ya san jimirinku. Ubangiji ya yi kusan zuwa.

6. Kada ku damu da kome, sai dai a kowane hali ku sanar da Allah bukatunku, ta wurin yin addu'a da roƙo, tare da gode wa Allah.

7. Ta haka salamar Allah, wadda ta fi gaban dukkan fahimta, za ta tsai da zukatanku da tunaninku ga Almasihu Yesu.

8. Daga ƙarshe kuma, 'yan'uwa, ko mene ne yake na gaskiya, ko mene ne abin girmamawa, ko mene ne daidai, ko mene ne tsattsarka, ko mene ne abin ƙauna, ko mene ne daɗɗaɗar magana, in ma da wani abu mafifici, ko abin da ya cancanci yabo, a kan waɗannan abubuwa za ku yi tunani.

9. Abin da kuka koya, kuka yi na'am da shi, abin kuma da kuka ji kuka gani a gare ni, sai ku aikata. Ta haka Allah mai zartar da salama zai kasance tare da ku.

10. Na yi farin ciki da Ubangiji ƙwarai da yake a yanzu kam, kularku gare ni ta farfaɗo, ko dā ma kuna kula da ni, dama ce ba ku samu ba.

11. Ba cewa, ina kukan rashi ba ne, domin na koyi yadda zan zauna da wadar zuci a cikin kowane irin hali da nake.

12. Na san yadda zan yi in yi zaman ƙunci, na kuma san yadda zan yi in yi zaman yalwa. A kowane irin hali duka na horu da ƙoshi da yunwa, yalwa da rashi.

13. Zan iya yin kome albarkacin wannan da yake ƙarfafa ni.

Karanta cikakken babi Filib 4