Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Filib 2:3-15 Littafi Mai Tsarki (HAU)

3. Kada ku yi kome da sonkai ko girmankai, sai dai da tawali'u, kowa yana mai da ɗan'uwansa ya fi shi.

4. Kowannenku kada ya kula da harkar kansa kawai, sai dai ya kula har da ta ɗan'uwansa ma.

5. Ku ɗauki halin Almasihu Yesu,

6. wanda, ko da yake a cikin surar Allah yake, bai mai da daidaitakar nan tasa da Allah abar da zai riƙe kankan ce ba,

7. sai ma ya mai da kansa baya matuƙa ta ɗaukar surar bawa, da kuma kasancewa da kamannin ɗan adam.

8. Da ya bayyana da siffar mutum, sai ya ƙasƙantar da kansa ta wurin yin biyayya, har wadda ta kai shi ga mutuwa, mutuwar ma ta gicciye.

9. Saboda haka ne kuma Allah ya ɗaukaka shi mafificiyar ɗaukaka, ya kuma yi masa baiwa da sunan nan da yake birbishin kowane suna,

10. domin dai kowace gwiwa sai ta rusuna wa sunan nan na Yesu, a Sama da ƙasa, da kuma can ƙarƙashin ƙasa,

11. kowane harshe kuma yă shaida Yesu Almasihu Ubangiji ne, domin ɗaukaka Allah Uba.

12. Saboda haka, ya ƙaunatattuna, kamar yadda a kullum kuke biyayya, haka kuma yanzu, ku yi ta yin aikin ceton nan naku da halin bangirma tare da matsananciyar kula, ba ma sai ina nan kawai ba, har ma fiye da haka in ba na nan.

13. Domin Allah shi ne mai aiki a zukatanku, ku nufi abin da yake kyakkyawan nufinsa, ku kuma aikata shi.

14. Kome za ku yi, kada ku yi da gunaguni, ko gardama,

15. don ku zama marasa abin zargi, sahihai, 'ya'yan Allah marasa aibu, a zamanin mutane karkatattu, kangararru, waɗanda kuke haskakawa a cikinsu kamar fitilu a duniya,

Karanta cikakken babi Filib 2