15. Ubangiji Mai Runduna zai tsare su,Za su tattake duwatsun majajjawa,Za su sha jini kamar ruwan inabi,Za su cika kamar tasar ruwan inabi,Kamar kuma kusurwoyin bagade.
16. A wannan rana Ubangiji Allahnsu zai cece su,Gama su jama'arsa ne, garkensa kuma,Kamar yadda lu'ulu'u yake haske a kambi,Haka za su yi haske a ƙasarsa.
17. Wane irin kyau da bansha'awa alherinsa yake!Hatsi zai sa samari su yi murna.Sabon ruwan inabi kuma zai sa 'yan mata su yi farin ciki.